#ArewaMuFarka
Akwai abin takaici idan muka dubi yanayin da yankinmu na Arewa yake zama koma baya kullum a bangarori da dama Kama daga zamantakewa, tattalin arziki, tarbiyya,tunanin me gobe ka haifar da Kuma kishin kanmu da yayayenmu masu tasowa.
Arewa da take kumshe da jiga-jigan kasarmu baki daya dasuke rike da madafun iko amma a kullum mune a gaba wajen tabarbarewar alamuran rayuwa baki daya. Mun zama marasa tunanin me gobenmu zata haifarmana ga yaranmu dake tasowa, an kaga mana talaucin dole da mutuwar zuciya da tumasanci.
Dattijan Arewa har yau babu jigo daya da kan iyayin magana da yawun Kare muradun Arewa dakuma farkar damu duhun da muke ciki dakuma inda muka dosa.
Yan siyasarmu an rasa jigon da zai tsaya tsayin daka wajen daura alumma akan turbar farfado da darajar Arewa da rayuwar yaranmu dake tasowa, an talauta matasanmu an kashe masu zuciya an daurasu akan turba marar bulewa.
Matasanmu mafi akasarinmu mun zama ragwaye babu abinda muka iya sai korafi da mallakar maganin matsalolinmu ba tareda mun ankara ba, gashi lokaci na kure mana batareda mun lura ba.
Babban abin damuwa idan na waiga na kalli yaranmu dake tasowa ta fannin tarbiyya da rashin sanin dalilin rayuwa da jahilci da yayimana katutu a kullum sai in hangi wai idan muka cigaba da tafiya haka nan da shekara goma masu zuwa wane yanayi zamu tsinci kanmu?
-Jahilici
-Talauci
-Ragwanci
-Rashin hadinkai
An rasa wadanda zasu kafa tubalin aniyar yaki dasu ba tare da wata mummunar manufa ba, mun mayar da kanmu marasa manufa a rayuwa har takai matsayin da yan yankinmu na kudu duk da makiyanmu ne a bayyane sunfimu hade kansu wajen nemawa kansu mafita a rayuwa suna amfani da duk wata gajerar dama dasuka samu wajen ganin sun taimaki nasu Kuma sun bayyana kiyayya ga duk wani Dan Arewa musamman Musulmi/Bahaushe mu Kuma sai neman suna da kokarin kyautata masu muna cutar da danginmu.
Sanin kowane cewa yankinmu na Arewa Yana fama da rashin tsaro da kashe kashe da Kuma Garkuwa da jamaa Amma mu da shugabanninmu munkasa mayarda muhimmanci wajen ganin bayan hakan sai gashi jihohin kudu sun kafa yansandan Sakai na jihohi (amotekun) domin samun Karin kariya a garesu duk da hakan bamuyi hankalin ko da kwaikwayarsu dukda mu yakamata ace sun kwaikwaya.
Zan cigaba inshaallahu
Sanusi Yau Mani
(National Comrade)
12/10/2020