Arewa Ina Mafita
#Arewa Mufarka 4
Hakika ya ishemu izina yanayin da muke ciki dakuma makomar da muke hange idan aka cigaba da tafiya haka.
bazanso in tsawaita rubutu na ba musamman ga yadda na fahimci a matsayin mu na matasa aikin mu yawuce rubuce rubuce da fadakarwa hakika muna bukatar shiga hidimar sauya shugabanci haikan izuwa shugabanci na gaskia wanda bashida bukatar sai ka daukarwa alumma alkawari aa saidai ka gamsar da alumma dalili da zaisa su zabeka su gani a kasa daga karshe su zama alkalan kansu.
Lokaci yayi da zamu fuskanci matsalolin da suke addabar mu mudaina wasa da hankalin junanmu wajen kakabawa wasu laifi, mudauka matsalar tamu ce kuma mu zamu gyara matsalar da kanmu.
Lokaci yayi da zamu daina siyasar Jam'iyya mukoma siyasar akida, manufofi dakuma dattaku na masu neman mu azasu a madafun iko.
Lokaci yayi da zamu daina zabar alumma ta hanyar dadin alkawuran da suke daukar mana mu koma zabar alumma a bisa gudunmuwar da suke bamu ko suka bamu a lokacin da suka samu wasu damarmaki.
Mu kalli tarin mabarata da suka tare a bakin tituna sunata gararanba a lokacin da yakamata ace kananan cikinsu suna makaranta, yara maza na cikinsu suna wajen koyan sanaa ko tareda iyayensu, iyaye matan da ke bara sunacan wajen fafutukar tarbiyyantar da yaran dasuka haifa, amma a karshe zasu kare ba ilimi, ba tarbiyya kuma ba madogara kuma muna tunanin zasu bar alumma su rayu a cikin aminci anan gaba?
Matasa mun kasance masu son hutawa da rayuwar birge wasu amma bamusan mu wahala ko kadan wajen neman nakai, balantana mu wahalar da kanmu wajen ganin alumma sun cigaba.
Lokaci yayi da zamu nemawa kanmu sauyi na gaskiya da gaskiya mu aje banbancin Addini, Akida, Jam'iyya, bangare ko nasaba mu rungumi alummar da zasu kawo mana cigaba na hakika wanda ba damuwarsu bace ace sunyi ko basuyiba.
Munsan wane hali muke ciki zuwa yau kuma mun siyasantar da matsalolinmu da kanmu kuma gashinan muna cikin yanayin da kowa zai iya bayani dakansa. Wasu bangaren muncigaba wasu bangaren kuma munsani.
Izuwa yanzu yakamata ace;
An wajabta karatu ga kowanenmu kuma an kirkiri hanyoyin samarwa kanmu madogara ko ba ta aikin gwamnati ba idan kuma hakan ya gagara to yazama kowa yanada hanya mai bulewa idan baisamu aiki bayan kammala karatu ba.
Ya Kamata ace a arewa muna da babbar Kasuwar dabbobi da zai bamu dama mutanen kudu suzo su sayi dabbobi a nan da kayan masrufi na abinci maimakon rashin imanin da suke mana ma konamu da kwacemana abinci da dabbobin da muka kaimasu kuma munkasa fahimtar zuwansu su saya wajenmu zaisa
1-Su fahimci darajarmu da kuma mune gatansu.
2-Musamu guraben aiki ga tarin alummar da suke zaune ba aikinyi
3-Mukara samun kudin shiga
4-Inganta tsaro da kuma kaunar juna.
Ya kamata ace mun fuskanci matsalar tsaro da tattalin arziki da take addabarmu mudaina daurawa juna laifi.
Ya kamata ace musan darajar kanmu mukuma himmantu wajen zama jigo ga yaranmu dake tasowa yanzu muzama gata a garesu mu share hawayensu muzama garkuwa garesu domin sui alfahari damu ranar da bamunan.
Hakika tara abin duniya, motoci da gidaje ba komai bane domin watarana hakan wasu zasu gajesu amma duka mutanen da muka share ma hawayensu muka zama ginshiki a garesu bazasu taba mantawa damu ba kuma muna cikin adduoinsu a kowane yanayi.
- Yan'uwa ina mafita?
Ya kamata mu farka.
Sanusi Yau Mani
(National Comrade)
Wed 14th July 2021